Dokar ingancin iska

Dokar ingancin iska

Dokokin ingancin iska na kula ne da matakin sarrafa fitar da gurɓatacciyar iska zuwa cikin sararin samaniya . Ƙarƙashin wannan ne aka shimfiɗa ƙa'idodin ingancin iska masu matuƙar ƙarfi don suna tsara ingancin iska a cikin gine-gine. Akasarin lokuta a na tsara dokokin ingancin iska ne musamman don a kare lafiyar ɗan adam ta hanyar iyakancewa ko kawar da yawan gurɓatacciyar iska. An gina wasu tsare-tsare don magance matsalolin muhalli masu faɗi, kamar iyakancewa akan sinadarai waɗanda ke shafar shingen gajimare, da shirye-shiryen tarfuwar hayaki don magance matsalar ruwan guba ko sauyin yanayi. Ƙoƙarin tsari sun haɗa da ganowa da rarraba gurɓataccen iska, saita iyakoki akan matakan da ake yarda da su, da fayyace fasahohin ragewa masu mahimmanci ko dacewa.


© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search